Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar CDU Ta Lashe Zabe A Jamus


Zaben Jamus: Shugaban Jam'iyyar CDU Friedrich Merz
Zaben Jamus: Shugaban Jam'iyyar CDU Friedrich Merz

Jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ta Jamus ta lashe zaben kasa da aka gudanar a ranar Lahadi, amma kuri’ar da aka kada ta bai wa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta AfD sakamako mafi kyau a matsayi na biyu.

Wannan sakamako ya sa shugaban masu ra’ayi mazan jiya Friedrich Merz ke fuskantar matsala a tattaunawar gwamantin hadin gwiwa.

Merz, wanda ba shi da gogewa ta rike wani ofis a baya, yana Shirin zama shugaban gwamnatin mai fama da matsalar tattalin arziki mafi girma a Turai, kawunan al’ummar ta sun rabu kan batun kaura da tsaronta dake tsakanin Amurka mai fito na fito da kuma Rasha da China masu kare muradunsu.

Bayan rugujewar kawancen da shugaba mai ci Olaf Scholz ke jagoranta, Merz mai shekaru 69 da haihuwa, dole ne ya kulla kawance daga majalisar dokokin kasar mai rarrabuwan kawuna a wani tsari da zai dauki lokaci.

Jam’iyyar sa ta masu ra’ayin mazan jiya da sauran manyan jam’iyyun sun yi watsi da yin aiki da jam’iyyar AfD, jam’iyyar da wasu jiga-jigan Amurka suka marawa baya cikin har da hamshakim attajirin nan Elon Musk.

Merz ya maida martani ga Amurka cikin kakkausar murya bayan nasarar da ya samu, inda ya soki wasu kalamai munana da ke fitowa daga Washington a lokacin yakin neman zabe, inda ya kwatanta su da tsoma baki daga Rasha.

“Don haka, muna fuskantar matsanancin matsin lamba daga barngarori biyu, amma babban abin da na sa a gaba a yanzu shi ne cimma hadin kai a Turai. Mai yiwuwa ne a samar da hadin kai a Turai,” in ji shi a wani taron tattaunawa da sauran shugabanni.

Zafafan kalaman Merz ga Amurka na zuwa ne duk da cewa shugaba Donald Trump ya yi maraba da nasarar da masu ra’ayin mazan jiya suka samu.

Trump ya rubuta a Truth Social cewa, “Kamar Amurka, jama’ar Jamus sun gaji da wata ajanda mara kan gado, musamman a kan batutuwan makamashi da shige da fice, da ke faruwa tsawon shekaru.”

Har yanzu ana ganin sa a matsayin mai goyon bayan hadin kai tsakanin Amurka da Yammacin Turai, Merz ya ce Trump ya nuna cewa gwamnatinsa ba ta damu da makomar Turai ba.

Merz ya kara da cewa “Abun zai fi bai wa fifiko shi ne karfafa Turai ciki sauri ta yadda za mu samu ainihin ‘yancin kai daga Amurka a hankali a hankali.”

Bayan yakin neman zaben da ya fuskanci tsaiko sakamakon kama mutane masu nasaba da bakin haure, jam’iyyar CDU/CSU ta masu ra’ayin mazan jiya ta lashe kashi 28.5 cikin 100 na kuri’un da aka kada, sai kuma jam’iyyar AfD da ta samu kashi 20.5 cikin 100, a cewar wani hasashe da gidan talabijin ZDF ya yada da misalin karfe 9:46 na yamma agogon kasar wato karfe (20:46 agogon GMT)

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG