Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mark Carney Ya Lashe Takarar Maye Gurbin Firai Minista Trudeau Na Canada


Mark Carney
Mark Carney

Carney mai shekaru 59 da haihuwa ya kayar da tsohuwar Ministar Kudi Chrystia Freeland wacce ta zo ta biyu a zaben wanda kimanin mambobin jam’iyyar 150,000 suka kada kuri’a.

Tsohon shugaban babban bankin Canada Mark Carney ya lashe zaben zama shugaban shugaban jam’iyyar Liberal Party mai mulkin ta Canada kuma zai gaji Justin Trudeau a matsayin firai minista, kamar yadda sakamakon ya bayyana a hukumance a ranar Lahadi.

Carney zai karbi mulki ne yayin da Canada ke cikin mawuyacin hali, kuma a lokacin rikicin kasuwanci da Amurka dadaddiyar kawarta kuma dole ne zai shirya babban zabe nan ba da dadewa ba.

Carney mai shekaru 59 da haihuwa ya kayar da tsohuwar Ministar Kudi Chrystia Freeland wacce ta zo ta biyu a zaben wanda kimanin mambobin jam’iyyar 150,000 suka kada kuri’a.

Trudeau ya sanar a watan Janairu da ya gabata cewa zai sauka daga mukamin sa bayan shafe sama da shekaru tara yana mulki yayin da farin jininsa ya yi kasa sosai, lamarin da ya tilastawa jam’iyyar Liberal Party ta gudanar da zabe cikin sauri don maye gurbin sa.

Carney, wanda ba shi da gogewa a siyasa, ya bayar da hujjar cewa, shi ne ya fi dacewa don farfado da jam’iyyar da kuma sa ido kan tattaunawar kasuwanci da shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke barazanar karin haraji da ka iya nakasa tattalin arzikin Canada wanda ya dogara da fitar da kayan kasashen ketare.

Carney shi ne kan gaba, wanda ya fi samun goyon baya daga ‘yan jam’iyyar da kuma tara kudi a cikin ‘yan takarar hudu na jam’iyyar ta masu sassaucin ra’ayi.

Nasarar da Carney ya samu ita ce karo na farko da wani bako a fagen siyasa da ba shi da cikakken tarihin siyasa ya zama firai ministan Canada.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG