Harin da aka kai Bannu a lardin Khyber Pakhtunkhwa ya raunata akalla mutum 32, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar. Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.
‘Yan bindigar sun tayar da wasu bama-bamai a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a harabar sansanin sojoji.
Galibi wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne yayin da gine-gine da suke kusa da su suka ruguje sanadiyyar karfin fashe-fashen.
Wasu majiyoyi sun ce an kashe akalla wasu ‘yan bindiga shida a wani artabun fadan bindiga.
Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton cewa, wata kungiyar ‘yan bindiga ta Jaish Al-Fursan ta dauki alhakin kai harin.
‘Yan bindigar sun sha auna Bannu a lokuta da dama.
A watan Nuwamban bara, wani harin kunar bakin wake da aka kai cikin wata mota ya halaka sojoji 12 tare da raunata wasu da dama a wani ofishin jami’an tsaro.
Dandalin Mu Tattauna