Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannayen Jari Sun Fadi A Wall Street


Kasuwar Hada-hadar Kudade Ta Wall Street
Kasuwar Hada-hadar Kudade Ta Wall Street

Kasuwar S&P 500 ta fadi da kashi 1.2 cikin 100 yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na hannayen jarin da aka rufe ya yi kasa. Kasuwar Dow Jones ta yi kasa da kashi 1.6 cikin 100.

Hannayen jari sun kara yin asara a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Wall Street a ranar Talata yayin da yakin kasuwanci tsakanin Amurka da manyan abokanan kasuwancinta ya karu, inda kasuwar S&P 500 ta rasa dukkan ribar da ta samu tun ranar zabe.

Gwamnatin Trump ta Sanya haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Canada da Mexico da ya fara aiki a ranar Talata da kuma rubanya karin haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga China.

Dukkan kasashen uku sun dauki matakan rama shirin saka haraji, lamarin da ya janyo damuwa kan tafiyar hawainiya na tattalin arzikin duniya.

Kasuwar S&P 500 ta fadi da kashi 1.2 cikin 100 yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na hannayen jarin da aka rufe ya yi kasa. Kasuwar Dow Jones ta yi kasa da kashi 1.6 cikin 100.

Kasuwar Nasdaq ta yi kasa da kashi 0.4 cikin 100.

Manyan kamfanonin fasaha sun dan fadi da kashi 10 cikin 100 daga mafi girman rufewarta na baya bayan nan, wanda shi ne abin da kasuwa ke la’akari da gyara, amma Nvidia, Microsoft da sauran manyan kamfanonin fasaha sun samu bunkasa inda suka taimaka wajen daidaita wadannan asarar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG