LeBron James ya zama dan wasan kwallon Kwando ta Amurka na farko a tarihi da ya zura kwallaye 50,000, idan aka hada da kwallayen da ya ci kafin da kuma lokacin kakar wasanni a daren ranar Talata.
James ya fara da wani bugu mai kyau da ya zura kwallo da maki 3 a farko zagaye na farko na wasan Los Angeles Lakers da New Orleans Pelicans.
James ya samu maki 49,999 a daren ranar Lahadi da ta gabata, lokacin da ya ci kwallaye 17 yayin da Lakers suka doke Clippers da ci 108-102 a karo na shida a jere.
James mai shekaru 40 ya riga ya zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin NBA a duk lokacin kakar wasanni da wasanni share fage a lokacin da yake murza leda a lokacin da sake rubuta dukkan ma’anar da suka gabata na tarihin kwallon Kwando.
James ya kai maki 50,000 a kakar wasannisa 22, wanda ake alakanta shi da Vince Carter na wanda ya fi taka leda a tarihin gasar NBA.
Shahararren dan wasan Lakers Kareen Abdul-Jabar, wanda ya buga kakar wasanni 20, shi ne a mataki na biyu a tarihin gasar NBA da maki 44,149.
Dandalin Mu Tattauna