Wakilin musamman da shugaba Donald Trump ya nada kan wadanda aka yi garkuwa da su, Adam Boehler, ya fada a ranar Lahadi cewa ganawar da ya yi da kunigyar Hamas da Amurka ta ayyan ta ta’addanci, a makon da ya wuce, game da wadanda ta yi garkuwa da su da take ci gaba da rike su a Gaza ta “taimaka kwarai da gaske” kuma za ta iya kai ga sako su “cikin makonni.”
Boehler ya shaida wa shirin ‘State of the Union’ na gidana talabijin din CNN cewa “Ina tsammanin za a samu yarjejeniya muddin aka sako dukkan wadanda aka yi garkuwa da su.”
Ya ce “Ina ganin akwai kwarin gwiwa.” “Kana ganin za a iya samun yarjejeniya ta dogon lokacin.”
Ana kyautata zaton cewa Hamas tana garkuwa da mutum 24 da ta kame a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, harin da ya janyo yakinta da Isira’ila.
Har ila yau, kunigyar na rike da gawarwaki wasu 34 da aka kashe ko a ranar farko na harin ko kuma yayin garkuwa da su, da kuma gawar sojan da aka kashe a shekarar 2014.
Boehler bai kore yiwuwar sake ganawa da kungiyar ta’addancin ta Fasaldinu ba.
Ganawar da wakilin ya yi da shugabannin Hamas, wadanda burinsu shi ne ruguza Isira’ila, ya zo ne kan adawar gwamnatin Yahudawa.
Boehler ya ce ya fahimci damuwar jami’in Isira’ila Ron Dermer ya nuna game da dangantakar Boehler da Hamas kai tsaye.
Boehler ya jaddada cewa, yana da manufa da take fili a tattaunawar, ta lalubo hanyar da za’a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da kuma kawo karshen yakin da aka kashe mutum 1,200 a harin farko na Hamas da Falasdinawa sama da 48,000 a hare-haren martani da Isira’ila ta kai.
Dandalin Mu Tattauna