Hadin gwiwa tsakanin masu shirya fina-finai na Isira’ila da Falasdinu ya biyo bayan hatsarin da dan gwagwarmaya Basel Adra ya fada ciki yayin da aka kama shi saboda yunkurinsa na tattara labarin baranar da sojojin Isra’ila ke yi wa garinsa da ke kudu da Yammacin Kogin Jordan, wanda dakarun Isira’ilan ke son amfani da shi a matsayin wurin horar da sojoji. Neman gafara da Adra ya yi ba a saurare shi ba har sai da ya yi abota da wani dan jarida Bayahuden Isira’ila wanda ya taimaka masa wurin bada labarin sa.
“Mun yi wannan fin ne a matsayin mu na Falasdinawa da Isira’ilawa, saboda idan muka hada kai, muryoyin mu sun fi karfi,” in ji dan jarida kuma mai shirya fina-finai Yuval Abraham. Ya yi amfani da jawabin amincewarsa wajen yin kira ga gwamnatin kasarsa kan abin da ya kira “mummunar lalata Gaza da al’ummarta.” Kuma ya yi kira ga Hamas da ta saki dukkan ‘yan Isira’ila da take garkuwa da su.
Shirin “No Other Land” ya kasance a cikin jerin shirye shiryen da suka kayatar a daren, bayan nasarar yin fice a bukin fina-finan. Sai dai shirin bai samu wanda za iyi kasuwancinsa a Amurka ba, bayan an rarraba shi a cikin kasashen 24. A bukin kyautar Oscar, ya doke “Porcelain War,” “Sugarcane,” “Black Box Diaries” da kuma “Soundtrack to a Coup d’Etat.”
An dauki shirin ne tsawon shekara hudu tsakanin 2019 zuwa 2023, inda aka kammala aikin kwanaki kafin Hamas ta kaddamar da mummunar harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kan Isira’ila da ya janyo aka fara yakin Gaza.
A cikin fim din, Abraham ya shiga cikin fadan al’umma da raba mutane da muhallan su, amma ya fuskanci turjiya daga Falasdinawan da ke nuna alfarmarsa a matsayinsa na dan Isira’ila. Adra ya ce ya kasa barin Yammacin Kogin Jordan kuma ana daukarsa kamar mai laifi, yayin da Abraham yake shigowa yana fita ba tare da tsangwama ba.
Dandalin Mu Tattauna