Ta yiwu ranar Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan wani kuduri da Birtaniyya ta gabatar da daftarinsa.
Shugaban Amurka Joe Biden da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ranar Alhamis, yayin da za su gana a Italiya a gefen taron kolin kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya.
An kama wasu mutane takwas daga kasar Tajikistan da ake zargin suna da alaka da kungiyar IS a Amurka a cikin 'yan kwanakin nan, a cewar wasu da ke da masaniya kan lamarin.
Sama da mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata gobara ta tashi a wani gini da ke dauke da kusan ma'aikata 'yan kasashen waje 200 a Kuwait, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Laraba.
Wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure ya nutse a yankin tekun Yemen, inda mutane akalla 49 suka mutu, yayin da wasu 140 suka bace, a cewar hukumar kula da baki 'yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira IOM a ranar Talata.
Wasu jami’an Amurka biyu sun ce shugaba Joe Biden ne ya amince da matakin tura makaman.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Sin, a yau Talata, ya ce, an kai wadanda suka jikkata asibiti, kuma babu wanda ke cikin mawuyacin hali.
Mataimakan alkalin jihar Delaware 12 ne suka samu dan shugaban kasar da laifi a tuhume-tuhumen aikata manyan laifuffuka 3 dake da nasaba da saye da mallakar bindiga lokacin da yake yawan ta’ammali da hodar iblis.
A yau Talata ne babban jami'in Hamas, Sami Abu Zuhri, da ke wajen Gaza ya ce ta amince da kudurin tsagaita bude wuta kuma a shirye take ta tattauna kan cikakkun bayanai.
Sojojin Isra'ila sun sake kai wani sabon hari a tsakiyar Gaza a jiya Lahadi, kwana guda bayan kashe Falasdinawa 274 a wani farmaki da suka kai da nufin ceto mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
A yanzu haka wasu mutanen Gaza sun koma shan ruwan lambatu mai najasa da kuma cin abincin dabbobi, a cewar Hanan Balkhy, darektan yankin gabas ta tsakiya ta Hukumar Lafiya ta Duniya tana mai rokon a kara kai dauki cikin gaggawa zuwa yankin da aka yi wa kawanya.
Kimanin mutane 63 ne aka yi musu bulala a bainar jama'a a lardin Saripul da ke arewacin kasar a ranar Talata, kamar yadda tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan (UNAMA) ta sanar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.