Mazauna Rafah sun ba da rahoton mummunar luguden wuta da harbin bindiga a yau Alhamis a birnin Gaza mai nisa da ke kudu bayan da Isra'ila ta ce ta kwace wata hanya mai mahimmanci a kan iyakar Falasdinawa da Masar.
Brazil ta janye jakadanta daga Isra'ila a ranar Laraba bayan shafe watanni ana takun saka tsakanin kasashen biyu dangane da yakin Gaza, wanda shi ne na baya-bayan nan daga wata kasa ta kudancin Amurka kan yakin da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu.
Shugaba Vladimir Putin ya gargadi kasashen yammacin duniya a ranar Talata cewa mambobin kungiyar tsaro ta NATO a Turai suna wasa da wuta ta hanyar bai wa Ukraine shawarar ta yi amfani da makaman kasashen yamma wajen kai hari a cikin kasarsa, lamarin da ya ce ka iya haifar da rikici a fadin duniya.
Jamus za ta ci gaba da barin tashar sufurin jiragen samanta na soji a Yamai a bude a mataki na wucin gadi, kamar yadda ma'aikatar tsaro a Berlin ta bayyana a yammacin jiya Talata, jim kadan bayan da Tarayyar Turai ta sanar da kawo karshen aikin soji a kasar nan da ranar 30 ga watan Yuni.
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza tun bayan harin na ranar 7 ga watan Oktoba ya sake farfado da yunkurin da duniya ke yi na a bai wa Falasdinawa kasar tasu.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya biyo bayan wata mummunar guguwa ta haddasa rugujewar wani katafaren rami a jihar Mizoram na kasar Indiya inda ya kashe mutane 12, kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana a jiya Talata.
Firaiminista Benjamin Netanyahu ya fada ranar Litinin cewa an yi "kuskure mai ban tausayi" a harin da Isra'ila ta kai birnin Rafah da ke kudancin Gaza, wanda ya kona wani sansanin da ke dauke da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, kuma a cewar jami'an yankin, akalla mutum 45 suka rasa rayukansu.
Kasuwanci tsakanin Isra'ila da Turkiyya ya sha fama da guguwar diflomasiyya cikin shekaru da dama da suka gabata, amma kuma ta ci gaba da gudana, inda ta kai biliyoyin daloli a shekara.
Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a wani sansanin jami’an tsaron Pakistan da ke kusa da kan iyaka da Afganistan da sanyin safiyar yau Litinin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar da wasu mahara biyar a wata musayar wuta da ta biyo baya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana bacin ransa a yau Litinin kan harin da Isra’ila ta kai kan sansanin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a Rafah, wanda jami’an Gaza suka ce sun kashe akalla mutane 45, tare da neman a tsagaita bude wuta nan take.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa a ranar Lahadi ta kara kiyasin adadin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Papua New Guinea zuwa sama da 670 yayin da masu ba da agajin gaggawa da ‘yan’uwansu suka yi fatali da fatan cewa za a sake samun wanda suka tsira.
Ma'aikatan kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce harin da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe akalla mutum 35 a ranar Lahadin da ta gabata tare da kai hari kan tantunan 'yan gudun hijira a kudancin birnin Rafah.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.