Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Amince Da Shirin Tsagaita Wuta A Gaza


United Nations Security Council votes on a ceasefire proposal
United Nations Security Council votes on a ceasefire proposal

A yau Talata ne babban jami'in Hamas, Sami Abu Zuhri, da ke wajen Gaza ya ce ta amince da kudurin tsagaita bude wuta kuma a shirye take ta tattauna kan cikakkun bayanai.

Hamas ta amince da kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ke goyon bayan shirin wajen kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, kuma ta shirye ta tattauna dalla-dalla, in ji wani babban jami'in kungiyar gwagwarmayar Falasdinu a ranar Talata a abin da sakataren harkokin wajen Amurka ya kira "alama mai cike da fata".

Za a ci gaba da tattaunawa kan shirin kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas a Gaza a ranar Talata da yamma, har zuwa ‘yan kwanaki biyu masu zuwa, kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a Tel Aviv bayan tattaunawa da shugabannin Isra'ila. "Ya zama wajibi mu yi wadannan tsare-tsare."

TOPSHOT - This handout photo released by the US State Department on June 10, 2024, shows US Secretary of State Antony Blinken (L) meeting with Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu in Jerusalem on June 10, 2024.
TOPSHOT - This handout photo released by the US State Department on June 10, 2024, shows US Secretary of State Antony Blinken (L) meeting with Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu in Jerusalem on June 10, 2024.

Blinken ya gana da jami'an Isra'ila a yau Talata a wani yunkuri na kawo karshen yakin da Isra'ila ta kwashe watanni 8 tana yi da Hamas wanda ya yi kaca-kaca da Gaza, kwana guda bayan shawarar da shugaba Joe Biden ya gabatar na sasantawa da kwamitin sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

A yau Talata ne babban jami'in Hamas, Sami Abu Zuhri, da ke wajen Gaza ya ce ta amince da kudurin tsagaita bude wuta kuma a shirye take ta tattauna kan cikakkun bayanai.

Ya rage ga Amurka ta tabbatar Isra'ila ta bi ta, in ji shi.

Ya ce Hamas ta amince da tsarin da ya tanadi janye sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma yin musanyar wadanda aka yi garkuwa da fursunonin Falasdinawan da Isra’ila ke tsare da su.

UN Gaza Human Rights
UN Gaza Human Rights

Shawarar Biden ta tanadi matakan tsagaita bude wuta da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su domin musanya da Falasdinawa da aka daure a Isra'ila, wanda a karshe zai kai ga kawo karshen yakin na dindindin.

Isra'ila dai ta ce za ta amince da dakatar da yakin na wucin gadi ne kawai har sai ta hallaka Hamas, yayin da Hamas ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar da ba ta ba da tabbacin kawo karshen yakin ba.

Amurka ita ce babbar aminiyar Isra'ila kuma babbar mai samar mata da makamai, ko da yake ta yi kakkausar suka kan yawan mace-macen fararen hula, da barna da kuma rikicin jin kai a Gaza da yakin sojin Isra'ila ya haddasa.

Sojojin Isra'ila sun kubutar da wasu mutane hudu da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, a wani samame da kwamandojin suka kai sansanin 'yan gudun hijira na birane da ke tsakiyar Gaza a ranar Asabar, inda Falasdinawa 274 suka mutu sakamakon harin bam da Isra'ila ta kai musu, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG