Akalla mutane bakwai ne aka kashe tare da yin garkuwa da 100 a daren Asabar bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Manoma a Najeriya na kokawa akan tashin farashin takin noma inda suke kira ga gwamnatin kasar da ta duba lamarin su, yayin da wasu masana ke cewa dole ne a dauki matakan gaggawa, yayin da damina ke kara shigowa gadan-gadan.
Jami'an tsaro a Najeriya sun sanar da samun nasarar kashe wani kasurgumin dan bindiga mai suna Alhaji Kachalla Ragas, wanda ya shahara wajen kai hare hare da kuma satar mutane domin neman kudin fansa a wasu sassan jihar Kaduna da jihohi makwabta.
Yau shekaru 30 da suka gabata, kwallayen da rashidi yekini da daniel amokachi da emmanuel amunike suka ci sun taimakawa tawagar super eagles yin bajinta a fitowarta ta farko.
Sanarwar da ofishin hukumar mai kula da yankin gabashin Tekun Maditereniyan ya fitar tace, an samu barkewar annobar ne daga ranakun 1 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan Mayun daya gabata.
A cewar wani kundin sauya fasalin aikin na Bankin Duniyan, gwamnatin Najeriya ta bukaci a tsawaita wa'adin kawo karshen aikin daga ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki, zuwa 31 ga watan Disamban badi.
A cewar rahoton masana a cibiyar Clingendael, kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin da aka yi ittifakin suna da alaka da al-qaeda suka rika tsallakowa daga yankin arewacin jamhuriyar Benin sun samu mafaka a gandun dajin gwamnati dake Kainji, daya daga cikin mafiya girma a Najeriya.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF na ci gaba da hada hannu da wasu hukumomi domin ceto rayukan dubban yara marasa gata, da kuma kyautata rayuwar su.
Hukuncin kotun na yau Alhamis ya rushe ko soke sanya hannu akan dokar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar da majalisar ta kammala aikinta akan daftarin dokar
Ranar 20, ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da 'yan gudun hijira suke ciki a sassan duniya.
Adadin wadanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya karu zuwa mutum 401, inda cutar tafi kamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.
A yau Alhamis, hadimin Shugaba Tinubu Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X cewar, Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da Bola Tinubu na Najeriya sun gudanar da tattaunawar kasa da kasa akan harkokin diflomasiya da tattalin arziki bayan kammala bikin rantsar da ramaphosan.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.