Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Ya Barke Tsakanin Fulani Da Al'umar Gomo A Karim Lamidon Jihar Taraba


'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya

Rikicin kabilanci tsakanin Fulani da kabilun Gomon ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

Mukaddashiyar kakakin rundunar 'yan sandar jihar Taraba, SDP Gambo Kwasha, ta tabbatar da faruwa rikicin da kuma asarar dukiyoyin masu yawa a yankin na Gomon da ke karamar hukumar na Karim Lamido.

Wani matashi wanda lamarin ya faru a idonsa ya shaidawa wakilinmu Lado Salisu cewa, rikicin ya fara ne sakamakon shiga gona da kuma barnar da shanun wani bafulatani suka yi, faruwar wannan lamari ne kuma ya sa mai gona ya fusata har lamarin ya kai ga kashe-kashe wanda ya zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

Ardo Jarenga Galdu, shugaban kungiyar Fulani ta Tapital Pulako Jonde Jam na kasa a tarayyar Najeriya, na daya daga cikin wadanda rikicin ya shafa.

Shi kuma Malan Usman Yakubu, da ke zaman shugaban kungiyar matasa kabilan Gomun, ya ce ba su ji dadin faruwar wannan lamarin ba kasancewar akwai kykkyawar fahimta tsakanin al'ummar Gomon da kabilar Fulani wanda ya kai ga kulla dangantakar auratayya tsakanin kabulun biyu.

A dalilin haka ya yi kira ga matasa daga duk bangarorin kabilan biyu da su yi hakuri kuma su guji daukar doka a hannunsu.

A saurari rahoton Lado Salisu Garba:

Rikici Ya Barke Tsakanin Fulani Da Al'umar Gomo A Karim Lamidon Jihar Taraba
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG