‘Yan majalisar sun hada da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).
A watan Disamban 2023, Majalisar Dattawa ta bayyana shirin gudanar da cikakken bincike a kan hukumar dake kula da fanshon sojoji.
Direba da ma’aikatan jirgin sun yi nasarar juya akalarsa zuwa filin jirgin saman Maiduguri tare da yin saukar gaggawa domin kaucewa bala’i.
Majalisar wakilai ta dauki wani mataki da wasu ke gani abin alheri ne bayan jin irin koke koken da suka rika tashi kan batun korar ma'aikata 1,000 da Babban Bankin Najeriya ya ce zai yi, yayinda kwararru a fanin tattalin arziki ke gani akwai bukatar kyakkyawan karatun ta natsu kan lamarin.
An sake samun tashin wata nakiya da ake zaton 'yan bindiga ne suka dasa ta a jihar Zamfara da wata Motar fasinja ta bi kai, ta kashe mutun biyu daga cikin matafiyan tare da jikkata wasu da dama daga cikin su.
Barau, wanda ya jagorancin zaman majalisar, yace kudurorin sun janyo cece kuce, inda yace an dorawa kwamitin alhakin tuntubar Antoni Janar na Tarayya, da bangaren zartarwa da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, hatsarin ya afku ne da kimanin karfe 10 na dare a kauyen Chelluri mai tazarar kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam dake jihar.
A yau Laraba, ‘yan bindiga suka dasa jerin sabbin nakiyoyi a yankin Mai Lamba na babbar hanyar Dansadau zuwa Gusau dake karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka hallaka matafiya.
Har yanzu tana kasa tana dabo kan wanda ya gina jerin gidajen da kotu ta mallakawa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa a birnin Tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin Najeriya da kudurorin ne makonnin da suka gabata.
Haka kuma Majalisar Dattawan ta dora wa kwamitocinta a kan kudi da albarkatun man fetur da iskar gas alhakin bincikar zarge-zargen rike kudade da kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya yi, ciki har da Naira tiriliyan 8.48 na tallafin man fetur, da dala biliyan 2 na kudaden harajin da ba a biya ba.
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.