Mutane 12, da suka hada da maza manya 10 da babbar mace 1 da karamar yarinya 1 sun mutu a wani hatsarin motar da ya faru a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam ta jihar Yobe a jiya Talata.
Kwamandan shiyar Yobe na hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya (FRSC), Livinus Yilzoom ne ya bayyana hakan a sanarwar daya rabawa manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.
A cewarsa, hatsarin ya afku ne da kimanin karfe 10 na dare a kauyen Chelluri mai tazarar kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam dake jihar.
A cewar Yilzoom, binciken farko ya nuna cewa tare hanyar da wata tifa kirar Howo tayi ne dalilin farko na afkuwar hadarin, yayin da gudun wuce sa’a da lodi fiye da kima suka kasance dalili na 2.
Ya kuma ja kunnen masu ababen hawa dasu kaucewa yin tafiya cikin dare saboda hatsarin raguwar gani sakamakon hazon da yanayin hunturu ke haddasawa.
Haka kuma kwamandan shiyar ya shawarci masu ababen hawa su kiyaye ka’idojin tuki a koda yaushe domin kaucewa afkuwar hakan a nan gaba.
Dandalin Mu Tattauna