Ya kuma jaddada cewa shawo kan wannan matsala zai samar da gagarumin rangwame a farashin kujerar aikin Hajjin 2025.
Shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Oyo, tare da iyalan dake alhinin rashin ‘ya’yansu.
A watan Nuwamban da ya gabata matatar mai zaman kanta ta rage litar fetur dinta zuwa N970.
Tinubu ya gabatar da daftarin kasafin kudin 2025 na Naira tiriliyan 49.7 a gaban zaman hadin gwiwar majalisun tarayya, inda ya warewa fannonin tsaro naira tiriliyan 4.9, ayyukan raya kasa naira tiriliyan 4.06, kiwon lafiya, naira tiriliyan 2.48 sai kuma ilimi da zai ci naira tiriliyan 3.52.
Kwacewar ta shafe wasu mashahuren mutane da kamfanoni 759 dake yankin Maitama II ta birnin Abuja, saboda rashin biyan kudin takardun mallakar filayen.
Gwamnan ya bayyana lamarin da ranar takaici ga gwamnatin jihar Oyo sannan ya jajantawa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu.
SP Osifeso ya tabbatar da mutuwar kananan yara maza da mata 35 a turmutsutsi da suka je makarantar Islamiyya da ke shiyar Bashorun a Ibadan don karbar kyaututtukan kirsimeti daga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola da, Oriyomi Hamzat waɗanda ake yi wa kallon haddasa al'amarin.
Wani rahoto da cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa, sama da mutane miliyan 2 ne aka yi garkuwa da su daga watan Mayun 2023 zuwa watan Afrilun 2024.
Adadin kasafin kudin Tinubu na 2025 na Naira tiriliyan 47.9 ya dara na 2024 da Naira tiriliyan 20.
Shugaba Tinubu ya bayyana aniyarsa ta sabunta tattalin arziki, inda ya godewa ‘yan Najeriya game da jurewar da suka nuna a tafiyar gwamnatinsa ta kawo sauyi a watanni 18 din da suka shafe tare.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayyar ta bar farashin lantarkin a yadda yake ga dukkanin rukunonin masu amfani da wutar.
‘Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki sakamakon yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi da rashin tabbas a kasuwar musayar kudade da ta sanya canjin dala kaiwa Naira 1, 700 a baya-bayan nan.
Domin Kari
No media source currently available