Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi karin haske a kan cewa babu sabon nau'in kwayar cutar korona samfurin XEC, da aka gano a Austireliya da wasu kasashen Turai a Najeriya.
Dokar ta soji ba ta bayyana wani dalili na korar Tambela ba, wanda aka nada matsayin firimiyan rikon kwarya jim kadan bayan Traore ya kwace mulki a watan Satumban shekara ta 2022.
Zaben kasar Ghana na kara karatowa, kuma kungiyoyin farar hula da na kasuwanci sai mika fatan alheri da burin a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana suke yi.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun mai alkalai 3, karkashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar, wanda ya bayyana dakatarwar da lamarin mai cutarwa kuma tauye hakkin Muhuyi Magaji ne na jin ba’asinsa.
A cewarsa, matakin soja bai wuce kaso 30 cikin 100 na abin da ake bukata wajen tabbatar da tsaron kasa ba, yayin da ragowar kaso 70 din ya dogara a kan matakan zamantakewar siyasa da tattalin arziki.
Gwamna Francis Nwifuru wanda ya bayyana hakan a jiya yace an tabbatar da mutane 48 daga cikin 394 sun kamu da zazzabin Lassa tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2024.
A cewar wata majiya a masarautar ta Kano, jami’an tsaro dauke da manyan makamai, ciki har da motocin sulke, sun yiwa kofar shiga fadar kawanya, tare da takaita zirga-zirga.
Hedkwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta kwato bindigogi sama da dubu takwas da dari biyu, da kuma sama da harsasai dubu dari biyu daga hannun 'yan ta'adda a baki daya sassa daban daban na kasar.
Kasar Amurka ta jaddada aniyar ci gaba da bayar da tallafi a Najeriya da kuma inganta shirin yadda zai kara kyautata rayukan 'yan kasar.
‘Yan majalisar sun hada da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).
A watan Disamban 2023, Majalisar Dattawa ta bayyana shirin gudanar da cikakken bincike a kan hukumar dake kula da fanshon sojoji.
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.