Bayan komawa zama a majalisar wakilan Najeriya a yau Alhamis, ‘yan majalisar 5 daga jam’iyyar Labour suka yi sauyin sheka zuwa jam’iyyar APC.
‘Yan majalisar sun hada da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).
Har ila yau, dan majalisa Erhiatake Sueno (daga jihar Delta) da ‘yar tsohon gwamnan Deltan James Ibori sun yi sauyin sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Tsaffin ‘ya’yan jam’iyyar Labour sun kafa hujja da rabuwar kanu a cikin jam’iyyar a matsayin babban dalilinsu na yin sauyin shekar.
Bbayan shafe shekaru fiye da 20 tana gwamgwarmaya, a matsayin wani bangare na kungiyar kwadago, jam’iyyar Labour tayi nasarar shiga fagen siyasar Najeriya a zaben 2023, inda ta samu kujerun sanatoci 6 da na ‘yan majalisar wakilai fiye da 34.
Dandalin Mu Tattauna