Mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun birnin tarayya Abuja ya yanke hukunci a ranar Litinin cewa, kadarorin da ke da alaka da wani tsohon babban jami’i, “ana zargin an same su da kudaden haram", sai dai bai ambaci sunan jami'in da aka ce ya mallaki gidajen ba, haka kuma ita ma Hukumar ta EFCC bata bayyana ubangijin gidajen ba.
A wata sanarwa da Hukumar ta fita jiya Talata da sa hannun kakakinta, Dele Oyewale ta bayyana cewa, bata fita fili ta fadi sunan jami'in da ake zargi da mallakar gidajen ba sabili da har yanzu ana kan gudanar da bincike.
Hukumar ta ce zata yi riga mallam masallaci idan ta shiga ambaton sunayen mutanen da ba a alakanta su kai tsaye da duk wata takardar mallakar kadarorin ba. Bisa ga cewar Hukunar, wanda ake zargi da mallakar gidajen ya musanta cewa nasa ne.
Hukumar ta bayyaca cewa, babu wanda take dauka a matsayin dan lele da ya fi karfin doka.
Hukumar EFCC ta fara daukar matakin kwace rukunin gidajen ne ta wajen garzayawa kotu inda ta sami wani umarni na wucin gadi ranar 1 ga Nuwamba na kwace kaddarorin.
I zuwa yanzu dai Hukumar bata fadi jami'in da take zargi da mallakar kaddarorin ba, sai dai kawai ta bayyana cewa, "wani tsohon babban jami’in gwamnati ne da EFCC ke bincike a kanshi a halin yanzu, ya gina gidajen."
Tuni wannnan batun ya karrade kafofin sada zumunta inda ake ta tafka muhawara kan ainihin wanda ya mallaki kaddarorin.
Dandalin Mu Tattauna