Majalisar Wakilai ta ba Babban Bankin Najeriya umurnin dakatarda sallaman ma'aikatan bankin 1,000 daya da ya yi niyya yi, domin ta Kafa Kwamiti na Musamman da zai yi bincike kan yadda za a yi wa ma'aikata 1,000 daya ritaya a lokaci daya kuma har za a biya su kudin sallama da ya kai Naira Biliyan 50 a wannan lokaci da kasar ke fama da rashin kudi.
Majalisar ta ce kwamiti ya yi bincike kan kai'doji da tsari da halarcin aikin.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan Majalisa mai wakiltan Yamaltu Deba ta Jihar Gombe Inuwa Garba ya yi karin haske cewa, Majalisa ita ce mai sa ido a yadda ake gudanar da mulki a kasa, saboda haka tana da hurumin daukan matakai kamar yadda doka ta tanada. Inuwa ya ce babu yadda za a yi Majalisa ta bari irin wadannan matakai suna faruwa ba tare da ta duba yiwuwar haka a bisa tsari ba, dalili ke nan inji shi, Majalisa ta kafa Kwamitin.
Shi kuwa masanin tattalin arziki na kasa da kasa, Yusha'u Aliyu ya yi tsokaci ne kan abinda CBN ya yi inda ya ce ba daidai ba ne a wayi gari a cikin wannan yanayi da kasa ke ciki, a yi wa mutane 1,000 daya ritaya haka kawai. Yusha'u ya ce ya kamata a bi tsarin aiki,da yawan shekaru da mutanen suka yi kafin a dauki matakin sallamar su, saboda a yi masu adalci wajen biyan su kudaden su yadda ya kamata..
A nashi bayanin, mai nazari kan al'amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, ya ce yanzu ne ya ke ganin kokarin 'yan Majalisa kan kokarin sauraren kokekoken al'umma. Abubakar ya ce wannan yunkuri na dakatar da sallaman wadannan ma'aikata sai an yi bincike, abu ne mai kyau, ga kuma batun dakatar da sauya fasalin harajin kasa da suka yi, duka wadannan abubuwa ne na yabo.
Majalisar ta ce ta dauki matakin ne domin bin kaidojin aikin gwamnati da kuma dokokin Kwadago.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna