Ya kara da cewar rahoton aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da aka gudanar a fadin jihar, ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi 6, 348 tare da alkintawa jihar Naira miliyan 314 a kowane wata.
A yau Talata, Majalisar Wakilan Najeriya ta yanke shawarar bincikar kwangilar samar da taraktocin 2, 000 da motocin girbi 100 da sauran kayayyakin noma da shirin gwamnatin Shugaba Tinubu na “Renewed Hope Agenda” ya gaza samarwa.
Shugaban kasar ya kara da cewa manufar kudurorin neman gyaran dokar harajin da ke gaban majalisar dokokin Najeriya ita ce daidaita adadin harajin da rage wa talakawan kasar nauyi da kara kason harajin da jihohi za su rika samu da kuma bunkasa harkokin kasuwanci ta hanyar samar da tallafi.
Wata matashiya 'yar shekaru talatin da uku, mai suna Changfe Maigari, ta kasance mace ta farko da ta zama mai tuka jirgin sama, a rundunar sojin ruwa ta Najeriya, tun kafa rundunar shekaru sittin da suka gabata.
An kashe akalla mutane uku, aka kuma kona gidaje da dama, da asarar dukiya mai yawa a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba sanadiyar wani rikicin cikin gida tsakanin mambobin Ekilisiyar United Methodist Church, wace ta sake suna ta koma Global Methodist Church.
A cikin ‘yan kwanaki da Kamfanin mai na Najeriya wato NNPCL ya rage farashin litar man fetur daga Naira dubu 1 da 60 zuwa Naira dubu 1 da 40, kungiyar IPMAN ma ta tabbatar da cewa, mambobinta sun rage kudin nasu mai da Naira 20 har zuwa 40.
gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tsarin sufurin jiragen kasa kyauta daga ranar 20 ga watan Disamban da muke ciki zuwa 5 ga watan Janairun 2025.
Daraktan yada labaran EFCC, Wilson Uwujaren, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a harabar ofishin hukumar dake Legas a yau Litinin yace an kama mutanen ne a Talatar data gabata 10 ga Disamban da muke ciki, a wani samamen ba zata da aka kai maboyarsu
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan yayin zaman Majalisar.
Manjo Janar Buba ya bukaci al’umma su yi watsi da labarai da rade-radin da ake yadawa a wasu kafafe.
A bisa kididdigar farko zuwa karshen wata kuwa, hauhawar farashin kayan abinci a watan Nuwamban 2024 ta kai kaso 2.98% abin da ke nuni da samun karin kaso 0.05% idan aka kwatanta da yadda yake a watan Oktoban 2024 (2.94%).
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.