Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Gwamnan Borno Da Fiye Da Fasinjoji 100 Sun Auna Arziki A Hatsarin Jirgin Sama


France Paris Air Show
France Paris Air Show

Direba da ma’aikatan jirgin sun yi nasarar juya akalarsa zuwa filin jirgin saman Maiduguri tare da yin saukar gaggawa domin kaucewa bala’i.

Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, da fiye da wasu fasinjoji 100 sun tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin jirgin sama sa’ilin da injin wani jirgin saman kamfanin Max Air ya kama da wuta jim kadan bayan daya tashi daga filin jirgin saman Maiduguri.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin jiya Laraba sa’ilin da jirgin saman, dake kan hanyarsu ta zuwa Abuja ya samu matsalar inji sakamakon yin karo da tsuntsu bayan mintuna 10 da tashi.

Direba da ma’aikatan jirgin sun yi nasarar juya akalarsa zuwa filin jirgin saman Maiduguri tare da yin saukar gaggawa domin kaucewa bala’i.

Wani ma’aikacin kamfanin Max Air, daya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da afkuwar lamarin da safiyar yau Alhamis.

An ruwaito ma’aikacin na cewar, “jim kadan bayan tashinsa, jirgin ya ci karo da tsuntsu a sama, abin da ya sanya daya daga cikin injinansa kamawa da wuta. nan take direban jrgin ya dauki matakin gaggawa domin ceton fasinjoji.”

Sai dai, nan take hukumar gudanarwar Max Air ta tura wani jirgin saman daga Kano domin yin jigilar fasinjojin, ciki harda mataimakin gwamnan zuwa Abuja.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG