A cewar bayanan dake shafin yanar gizon ofishin jakadancin, ziyarar farko za ta kunshi “nazarin takardun da mutum ya gabatar” tare da jami’in karamin ofishin jakadancin. Ziyarar ta 2 za ta kasance ganawar neman bizar da kanta,
A cewar Sarkin babu wata sanarwa a hukumance dangane da dalilin daukar matakin.
An kama wanda ake zargin ne yayin sintirin yau da kullum akan babbar hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Kankara a ranar 19 ga watan Nuwamban daya gabata a karamar hukumar Danmusa ta jihar.
Kamfanin yace rushewar babban layin lantarkin ta faru ne da misalin karfe 1 da mintuna 33 na ranar yau, Laraba, abin da ya sabbaba daukewar lantarki a dukkanin layukan rarraba wutar.
An ce faruwar lamarin ta haddasa gagarumin tsaiko, inda aka jinkirta tashin jirage da dama yayin da hukumomi ke kokarin yin gyara a kan titin tashin jiragen da al’amarin ya faru.
Ta bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da take jawabi a gangamin Najeriya na yaki da tarin fuka na 2024 daya gudana a Abuja.
Bayan zamansa a Abuja, zai zarce zuwa Legas, inda zai gana da wakilan ‘yan kasuwa, tare da ziyartar wata cibiyar kyankyasar fasahohi da kuma ganawa da mambobin bangaren al’adun Najeriya da kungiyoyin farar hula, irinsu Dr. Nike Okundaye da Farfesa Wole Soyinka.
Mai Shari'a Maryam Anenih ta kotun tarayya dake Abuja, tasa kafa tayi fatali da bukatar neman belin da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya gabatar.
Tsawon mako 2 kenan da kudin Naira ke samun tagomashi a kasuwar musayar kudade a kasar, inda ake musayar kudin akan kasa da Naira 1,570 a kowacce dalar Amurka, maimakon Naira 1,740 da yake a baya, kuma wannan shine karo na farko da kudin Naira ya samu irin wannan tagomashi a shekarar 2024.
Jami’in dake jagorantar NHRC a jihar yobe, Labaran Babangida, ne ya bayyana hakan yayin bikin zagayowar ranar kare hakkin dan adam ta duniya ta bana a birnin Damataru, fadar gwamnatin jihar Yobe.
Yayin zaman kotun, lauyoyin masu kara, Mukhtar Ahmad da Shamsudeen Saka sun gabatarwa kotun da shaidu 3 da dimbin takardu a matsayin hujjar hukumar EFCC a kan wadanda ake kara.
Cibiyar da na’urorin dake cikinta zasu “tsayar da mizanin amfanin da fasaha wajen sanya idanu akan iyakokin kasa domin tabbatar da tsaronta.”
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.