A watan Nuwamban 2023, ma’aikatar gona da tabbatar da wadatar abinci ta tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniyar shekaru 5 da wani kamfani mai zaman kansa ta samar da taraktoci 2, 000 da motocin girbi 100 da sauran kayan noma a duk shekara, wanda jumlar kudin ta kama fiye da dala milyan 70 da naira bilyan 2.9.
Ana sa ran yunkurin gwamnatin tarayyar ya rage yawan hauhawar farashin kayan abinci ta hanyar kara yawan abincin da ake nomawa tare da rage yawan kashe kudin musaya wajen sayen kayayyakin da aka riga aka kera sakamakon bunkasar samar dasu a cikin gida.
Sai dai abin takaici, shekara guda bayan kulla yarjejeniyar ko tarakta daya ba’a samar ba.
Dandalin Mu Tattauna