Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Kamfanin NNPC Kawai Ya Rage Farashin Litar Mai Ba - IPMAN


Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a birnin Lagos, bayan da aka cire tallafin mai.
Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a birnin Lagos, bayan da aka cire tallafin mai.

A cikin ‘yan kwanaki da Kamfanin mai na Najeriya wato NNPCL ya rage farashin litar man fetur daga Naira dubu 1 da 60 zuwa Naira dubu 1 da 40, kungiyar IPMAN ma ta tabbatar da cewa, mambobinta sun rage kudin nasu mai da Naira 20 har zuwa 40.

Shaidun gani da ido da dama sun tabbatar da cewa, Kamfanin NNPCL ya rage Naira 20 kan kowacce litar mai a sassa daban-daban na birnin tarayya Abuja.

Bayanin Ibrahim Isa, wani mai abin hawa da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya tabbatar da cewa, gidajen man kamfanin NNPCL na aiwatar da sabon farashin da aka rage, labarin da ya yi ta yaduwa a kafoffin yada labalai na yanar gizo.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

A nashi bayanin, Aliyu Muhammad Tukur, ma’aikaci a gidan man Azman ya shaida wa Muryar Amurka cewa, suna rage nasu farashin ne sakamakon yanayin rashin samun kasuwa.

Sai dai wasu ‘yan kasar sun ce matakin rage farashin litar mai da kamfanin NNPCL ya dauka ya nuna rashin tausayin talakawa ne kawai ganin irin gagarumin sauyin da aka gani a kasa da shekaru biyu a farashin kowacce litar mai a Najeriya.

Wani jigo a a kungiyar IPMAN Dakta Zarma Mustapha ya ce rangwame da aka samu a kudin sauke kaya na daga cikin dalilan da ya kawo ci gaban da aka samu ya na mai tabbatar da cewa, ba gidajen man NNPC kawai suka rage farashi ba, har ma da mambobin kungiyar su ta IPMAN wanda nasu ragin ke tsakanin Naira 20 zuwa 40.

Layin Mai a gidan man NNPC Mega Station na Makurdi, Jihar Binuwai, Najeriya (Tijjani Mohammed)
Layin Mai a gidan man NNPC Mega Station na Makurdi, Jihar Binuwai, Najeriya (Tijjani Mohammed)

Dangane da bambanci tsakanin farashin dauko mai daga matatar man Dangote da na NNPCL, Dakta Zarma Mustapha ya ce suna dauko kaya daga matatar Dangote a kan Naira 970 kowacce lita a bisa sharadin sayen lita miliyan biyu.

Wasu majiyoyi masu karfi da suka bukaci a sakaya sunan su sun ce man kamfanin NNPCL ya fi na matatar Dangote tsada.

Sauye-sauye a farashin litar man fetur a cikin kasa da shekaru biyu a Najeriya dai na ci gaba da jefa talakawa cikin matsi sakamakon wasu abubuwa da suka hada da cire tallafi, matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka a ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki lamarin, da masana tattalin arziki suka ce ya jefa ‘yan kasar cikin wani rin munin tsadar rayuwa.

Saurari cikakken rahoton:

Ba Kamfanin NNPC Kawai Ya Rage Farashin Litar Mai Ba - IPMAN
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG