Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ta Karu A Watan Nuwamba


Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

A bisa kididdigar farko zuwa karshen wata kuwa, hauhawar farashin kayan abinci a watan Nuwamban 2024 ta kai kaso 2.98% abin da ke nuni da samun karin kaso 0.05% idan aka kwatanta da yadda yake a watan Oktoban 2024 (2.94%).

Jumlar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta karu zuwa kaso 34. 60 cikin 100 a watan Oktoban 2024, a cewar hukumar kididdigar kasar (NBS) a yau Litinin.

Hauhawar farashin ta watan Nuwamban ta bayyana samun karin maki 0.72 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Oktoban 2024, a cewar rahoton alkaluman auna farashin kayayyakin masarufi (CPI) na NBS na baya-bayan nan da ke auna yanayin sauyawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.

“A bisa kididdigar yadda farashin kayayyaki kan sauya daga farko zuwa karshen shekara kuwa, jumlar hauhawar farashin kayayyakin ta karu da kaso 6.40 cikin 100 a kan wacce aka gani a watan Nuwamban 2024 ( 28.20%).

Hakan na nuni da cewar jumla hauhawar farashin kayayyakin (a bisa kididdigar farko zuwa karshen shekara) ya karu a wata Nuwamban 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a irin wannan watan a shekarar da ta gabata (Nuwamba 2023),” a cewar NBS.

Haka kuma, farashin kayan abinci a watan Nuwamban 2024 ya kai kaso 39.93% a bisa kididdigar farko zuwa karshen shekara, inda ya karu da kaso 7.08% a kan yadda yake a watan Nuwamban 2023 (32.84%).

A bisa kididdigar farko zuwa karshen wata kuwa, hauhawar farashin kayan abinci a watan Nuwamban 2024 ta kai kaso 2.98% abin da ke nuni da samun karin kaso 0.05% idan aka kwatanta da yadda yake a watan Oktoban 2024 (2.94%).

An alakanta hauhawar farashin ne da karuwar farashin kayayyakin masarufi irinsu danye da bushashen kifi tarwada da kifi saidin da shinkafa da garin doya da gero da garin masara da kwan kajin turawa da garin madara da danyar madara da bushashen naman saniya da naman akuya da daskararren naman kaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG