Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin dake cewa rundunar sojin Faransa na shirin kafa sansani a Najeriya.
Sanarwar da daraktan yada labaran shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce karin hasken ya zamo wajibi sakamakon rahotannin da ake yadawa, na cewa sojojin Faransa sun riga sun sauka a kasar.
“An ja hankalin shelkwatar tsaro game da rahotannin yanar gizo dake zargi game da isowar ayarin farko dakarun Faransa a birnin Maiduguri da nufin kafa sansanin soajan Faransa a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
“Da kakkausar murya rundunar sojin Najeriya ke sanar da cewar babu kamshin gaskiya a wannan labari kuma ba komai illa tsagwaron karya da makirci.
Manjo Janar Buba ya bukaci al’umma su yi watsi da labarai da rade-radin da ake yadawa a wasu kafafe.
Dandalin Mu Tattauna