Wani wanda lamarin ya rutsa da shi, da Muryar Amurka ta zanta ya bayyana cewa, wadanda suka tada hankalin sun ruske su lokacin suna ciki sujada, suka fara tada hankali a kone-kone da ya yi sanadin mutuwar kanensa da wadansu kananan yara biyu .
Shikuwa Simon munga Shugaban matasan Ilikisiyar ya bayyana cewa, jami'an tsaro da aka girke a Cocin ne su ka sa lamarin bai yi muni a Majami'ar da su ka fara kai hari ba, kasancewa jami'an tsaro sun hana su shiga harabar Majami'ar lokacin sujada.
SP Usman Abdullah Jada kakakin rudunar 'yan sandan jihar Taraba ya tabbatar da faruwan rikicin da mutuwar mutane uku, da kuma asarar dukiya masu yawa a karamar hukumar Karim Lamido sakamakon wanan al'amari.
Ya bayyana cewa, an tura jami'an 'yan sanda wurin domin kwantar da rikicin da kuma kiyaye doka da oda.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna