Fashewar da tayar wani jirgin saman dakon kaya mallakin kamfanin Allied Air ta yi, ya sabbaba kaucewarsa daga kan titinsa mai lamba 22 a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a yau Laraba.
Jirgin saman na dauke da fasinjoji 5 a cikinsa, a cewar sanarwar da hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) ta fitar.
Jami’a mai magana da yawunFAAN, Obiageli Orah, ta ce an yi nasarar kubutar da fasinjojin tare da garzayawa dasu zuwa asibiti domin samun kulawa.
Ta kara da cewa filin saukar jiragen saman ya rufe titin jirgin na dan wani lokaci saboda faruwar lamarin.
An ce faruwar lamarin ta haddasa gagarumin tsaiko, inda aka jinkirta tashin jirage da dama yayin da hukumomi ke kokarin yin gyara a kan titin tashin jiragen da al’amarin ya faru.
Dandalin Mu Tattauna