Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya isa fadar gwamnatin Najeriya a ziyarar daya kaiwa Shugaba Tinubu a yau Laraba, bayan daya sauka a kasar a jiya Talata.
Da isarsa kasar a jiya, ya samu tarba a bangaren shugaban kasa na filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, daga Ministan Babban Birnin Tarayyar, Nyesom Wike.
Ana sa ran Steinmeier, wanda aka tsara ziyararsa a Najeriya ta kai har 12 ga watan Disambar da muke ciki, ya gudanar da wasu jerin ayyuka irinsu ganawa da Shugaba Tinubu da kuma shugaban kungiyar ECOWAS, ta bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, Alieu Omar Touray.
Bayan zamansa a Abuja, zai zarce zuwa Legas, inda zai gana da wakilan ‘yan kasuwa, tare da ziyartar wata cibiyar kyankyasar fasahohi da kuma ganawa da mambobin bangaren al’adun Najeriya da kungiyoyin farar hula, irinsu Dr. Nike Okundaye da Farfesa Wole Soyinka.
Zai kuma samu damar kewaya birnin Legas domin fahimtar yadda babban birnin ke bunkasa, ciki har da kalubalen muhalli da na zamantakewa.
Dandalin Mu Tattauna