Kotun ta yi fatali da bukatar belin ne bisa hujjar cewa, an shigar da bukatar neman belin kafin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa( EFCC) ta tsare tsohon gwamnan wanda hakan ya sabawa sharudan bayar da belinsa.
Tsohon gwamnan yana fuskantar tuhuma tare da wadansu mutane biyu, Umar Shu'aibu Oricha da Abdulsalam Udu, kan aikata laifin almundahana da kudin da ya kai Naira biliyan dari da goma, da hukumar cin hanci da Rashawa-EFCC ta gabatar kansa.
Da yake gabatar hujjar neman beli, lauyan da ke kare tsohon gwamnan, Joseph Daudu, SAN, ya ce. Bello zai kiyaye belin.
Sai dai Mai Shari'a Maryam Anenih ta ce, bisa tsarin kotu, ba a kai ga lokacin gabatar da bukatar belin ba, sabili da akwai wadansu matakai da lallai ne a bi su a tsarin kotun kafin a fara batun neman belin wanda ake tuhuma.
Da yake tsokaci kan fatali da bukatar belin da kotu ta yi, wani lauya mai zaman kansa, Barrister Sanusi Ibrahim Sanusi, yace kotun tana da 'yancin daukar wannan matakin duk da yake zargi ne ba a tabbatar da aikata laifin ba, ya ce nan gaba lauyar wanda ake karar zai sake iya gabatar da bukatar idan kotu ta gamsu ta bada belinshi.
Saurari cikakken rahoton Ahmed Muhammed Danasabe:
Dandalin Mu Tattauna