Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya sake rugujewa a karo na 12 cikin shekarar 2024 da muke ban kwana da ita.
Sakon da aka wallafa a shafin X na babban layin lantarkin Najeriyar ya tabbatar da cewa layin ya rushe da misalin karfe 2 da mintuna 9 na ranar yau Laraba.
“Babban layin lantarkin ya rushe kuma yanzu za’a fara aikin gyaransa,” kamar yadda aka wallafa a shafinsa na X.
Haka kuma sanarwar da kamfanin rarraba hasken lantarki na Jos ya aikewa abokan huldarsa ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Kamfanin yace rushewar babban layin lantarkin ta faru ne da misalin karfe 1 da mintuna 33 na ranar yau, Laraba, abin da ya sabbaba daukewar lantarki a dukkanin layukan rarraba wutar.
“Muna fatan dawowa abokan huldarmu da hasken lantarki kamar yadda suka saba da zarar babban layin lantarkin na kasa ya koma aiki.” kamar yadda shugaban sashen yada labaran kamfanin rarraba lantarkin Jos, Dr. Friday Elijah ya shaidawa abokan huldarsu.
Daga watan Janairu zuwa Nuwambar 2024 babban layin lantarkin ya rushe sau 11, inda russhewar ta yau ta zama ta 12.
Dandalin Mu Tattauna