Akalla mutane 100 ne, akasarin su mata suka bace, bayan da jirgin ruwan dake dauke da su zuwa wata kasuwar hatsi, ya nutse a ruwa, a yankin kogin Naija dake Arewacin Najeriya, cewar mahukunta a ranar Juma’a.
NNPCL) ya yi karin haske a kan cewa tsohuwar matatar man Fatakwal mai karfin tace ganga 60, 000 a kowace rana da aka farfado da ita a kwanakin nan na aiki ne a kan kaso 90 cikin 100, ba kaso 70 cikin 100 ba kamar yadda kungiyar masu gidajen mai ta Najeriya (PETROAN) ta bayyana ba.
Wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan hulda jama’a na bataliyar, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma ta ce kamen nasa nada nasaba da samamen da ake gudanarwa a yankin Neja Delta na yaki da satar danyen mai.
A baya an yi ta wasan buya tsakanin Bello da hukumar EFCC da ta shigar da karar shi kan zargin wawure kudaden jihar ta Kogi - zargin da ya musanta.
Yahaya Bello wanda ya yiwa kotun jawabi da kansa, ya shaidawa mai shari’a Emeka Nwite cewa an sanar da shi game da batun gurfanarwar ne a kurarren lokaci a jiya Alhamis 28 ga watan Nuwamban da muke ciki don haka bai samu damar sanar da lauyoyinsa ba.
An tsamo gawawwaki 8, yayin da ake ci gaba da aikin ceto domin gano ragowar fasinjojin.
Okonjo-Iweala ita ce mace kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami tunda aka kafa kungiyar.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana yunkurin samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt 14,000 ta hanyar amfani da madatsun ruwa, lamarin da masana ke cewa gwamnatocin baya sun sha daukar irin wannan alkawarin, amma a karshe kuɗaɗen da ake warewa ke salwanta.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shaidawa ‘yan kasuwar Faransa cewa kasarsa na maraba da harkokin kasuwanci, inda yace gwamnatinsa na samar da kyakkyawan yanayin da zai taimaka musu cin nasara.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce binciken da ta yi kan yadda hukumomin Najeriya, suka murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Agusta, ya nuna cewa jami’an kasar sun kashe akalla masu zanga-zangar 24 tare da tsare wasu fiye da 1,200.
An sake zaben Adefunke Adeyemi a matsayin babbar sakatariya a hukumar kula da sufurin jiragen saman Afirka (AFCAC) a yayin karo na 35 na babban taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin Brazzaville, na Congo.
Yayin mika rahoton, shugaban kwamitin Babajimi Benson, yace Laftanar Janar Oluyede ya cika dukkanin bukatu.
Domin Kari
No media source currently available