A yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024 ne al'ummar jihar Ondo za su zabi sabon gwamnan da zai jagorance su.
An binne gawar ne da misalin karfe 4.41 na yammaci bayan wani biki da aka shafe fiye da sa’o’i 2 ana gudanarwa.
An dakatar da alkalan 2 ne tsawon shekara guda ba tare da albashi ba sannan za’a cigaba da sanya idanu a kansu tsawon shekaru 2 a nan gaba.
Hukumar ta alakanta tashin farashin da karuwar kudin sufuri da farashin kayan abinci.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Sadiq shima ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Kotun kolin ta kori karar ne saboda rashin wadatattun hujjoji.
Kungiyar Kamfanoni A Najeriya (MAN) ta bayyana cewa, tana fuskantar barazanar durkushewa, kasancewa a yanzu haka, kayayyakin da suke sarrafawa a kasar na zamo musu kwantai sakamakon tsadar kayan sarrafawa.
Masaan sun ce akwai bukatar kyakkyawan nazari kan hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya, biyo bayan bayanin da Ministan Makamashi Adebayo Adelabu yayi cewa, Najeriya ana bukatar 'yan kasuwa su zuba jarin dala biliyan 10 domin a shawo kan matsalar wutar lantarki a kasar.
A cewar NNPCL, hadin gwiwar wani muhimmin mataki ne na tabbatar da nasarar dorewar ayyukan matatar ta Dangote tare da inganta amfani da iskar gas a cikin Najeriya.
Wadanda suka mutun sun hada da maza 3 da wata mata mai shekaru 32 dake shirye-shiryen yin aure.
Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce a ranar Alhamis ya kara yawan man da ake hakowa zuwa ganga miliyan 1.8 a kowace rana tare da yiyuwar adadin ya kai miliyan biyu a karshen shekara
Egbetokun ya kuma ce za’a takaita zirga-zirgar dukkanin ababen hawa a kan tituna da hanyoyin ruwa da sauran nau’ukan sufuri tun daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranar Asabar mai zuwa a fadin jihar in banda masu ayyukan musamman.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.