A yau Litinin ne Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da yaki da mabarata, inda ya bayyana cewa jami'an tsaro za su fara kama su daga yau idan sun sake fitowa bara a titunan babban birnin.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a yau Litinin, direban bolt Stephen Abuwatseya ne ya shigar da korafi kan batun ga rundunar.
Ganawar wani bangare ne na kokarin da kungiyar gwamnonin arewa ke yi na tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin dake damun yankin musamman matsalar tsaron da taki ci taki cinyewa, da talauci da yara marasa zuwa makaranta da sauran kalubalen zamantakewar dake addabar yankin
Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma'aikatan Da Ba Malamai ba (NASU) sun fara wani yajin aikin gamagari domin neman a biyasu kudaden albashin da suke bi bashi.
Kamfanin na TCN ya kore wasu rahotannin da ke nuni da cewa babu ranar kammala aikin gyaran wutar.
Jaridar kwallon kafa ta France Football ce ta kirkiri ba da wannan lambar yabo a shekarar 1956 don karrama dan kwallon da ya fi nuna bajinta a fagen tamaula.
Sarakuna da Hakimai akalla goma sha uku ne suka yi murabus daga mukaman su a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ya jima yana fama da matsalolin rashin tsaro.
Zaben kananan hukumomi da aka yi a ranar sabar a jihar Kano ya gamu da kalubalen rashin fitowar jama’a rumfunan zabe.
Zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Kano yau asabar, 26 ga watan Oktoba na 2024, ya gamu da kalubalen rashin fitowar Jama’a domin kada kuri’a kuma Jami’an tsaro musamman ‘yan sanda su ma basu fito aikin bada tsaro ba.
Kamapanin bada wutar lantarkin ya ce 'yan ta'adda ne ke lalata hanyoyin bada wutar lantarki. Lamarin da ya jefa yankin arewacin Najeriya cikin duhu tsawon kwanaki.
Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya na Najeriya (JOHESU) ta ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7, tun daga tsakad daren yau Juma’a.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.