An sallame shi saboda zargin aikata almundahana.
Kudirin neman yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima da kuma samar da damar yin zabe daga wajen kasar ya tsallake karatu na 2 a Majalisar Wakilai a yau Laraba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wani tsoho dan Jamhuriyar Nijar mai shekaru 58 da haihuwa da ake zargi da safarar makamai daga kasar Aljeriya zuwa Najeriya tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda 16.
Duk da cewa babu tabbatarwa a hukumance game da yawan mutanen da suka mutu, majiyoyi sun ce an hallaka kimanin sojoji 20.
MDCAN ta kara da cewar mutum 1, 799 daga cikin mambobin nata, kwatankwacin kaso 29.31 cikin 100, na tsakanin shekaru 55 da haihuwa zuwa sama a yayin da kaso 1 bisa 3 na adadin ke shirin yin ritaya nan da shekaru 5 masu zuwa.
Kwamishinan lafiya ta jihar, Hajiya Asabe Balarabe wacce ta bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto, tace a halin yanzu jihar na bada kulawa ga mutane 15 da suka kamu da cutar.
Matukar aka amince, za’a yi amfani da rancen wajen cike gibin Naira tiriliyan 9.7 dake cikin kasafin kudin na bana.
A sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi, shugaban kasar Angola Joao Lourenco, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga” iyalan da mummunan hatsarin ya shafa kai tsaye.
A wani martani da ya mayar nan take ta hanyar jerin sakonnin Twitter, mashawarcin Shugaba Tinubu akan hulda da jama’a, Sunday Dare, yace tsohon shugaban kasa Obasanjo bashi da mutuncin da zai soki gwamnatin Bola Tinubu.
An danganta wannan katafaren ci gaban da aka samu galibi ga karuwar yawan danyen man da ake fitarwa, wanda ya karu daga ganga miliyan 1.131 a 2022 zuwa ganga miliyan 1.41 a kowace rana a 2023.
A yau Litini, shugabannin kungiyar G-20 ta kasashen 20 mafi karfin arziki a daniya sun fara hallara a kasar Brazil domin sake farfado da tattaunawa akan sauyin yanayi wacce ta cije a baya tare da shawo kan bambance-bambancen dake tsakaninsu dangane da rikicin gabas ta tsakiya da yakin Ukraine.
Kudirin sabon fasalin gyara tsarin haraji da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kudura aiwatarwa a Najeriya, ya janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar, musamman masu ruwa da tsaki da ma 'yan kasuwa.
Domin Kari
No media source currently available