Mai yuwuwa ne wasu kananan yara su 29 su fuskanci hukuncin kisa a Najeriya, bayan da aka gabatar da su a gaban kotu a ranarJuma’a, bisa laifin shiga zanga zangar tsada da matsin rayuwa da aka yi a kasar.
A taron Majalisar ƙolin tattalin arzikin kasar karo na 144 ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, Gwamnati ta yi kira ga waɗanda suke ajiye da dalar Amurka a gidajensu ko wasu wurare dake wajen kasar da su hanzarta kai kuɗaɗen bankunan kasar kafin nan da watanni 9
Bayan da aka sauke shi da karfin tsiya daga jirgin, shahararren dan daudun ya wallafa al’amarin a shafinsa na instagram domin sanar da masu bibiyarsa halin da ake ciki.
Ana tuhumar mutanen, su 75 da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 12 da 15 da laifuffukan da suka shafi ta’addanci guda 10, da suka hada da yunkurin kifar da gwamnati da kuma zargin yin tawaye sakamakon rawar da suka taka a zanga-zangar gamagari.
Rahotanni sun ce gwanayen ninkaya ne suka gano baraguzan jirgin a lokacin da hukumar ta NSIB take jagorantar ayyukan ceto.
Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun yi fatali da kudirin, musamman gyaran da ake shirin yi a kan sauya tsarin rabon harajin sayen kayayyaki (vat) zuwa wanda zai rika la’akari da asalin inda kayan ya fito.
An sace Dr. Papoola, wacce ta kasance magatakarda a fannin kula da lafiyar idanu na cibiyar, tare da mijinta, Nurudeen Papoola, wanda hafsan soja ne da dan danuwanta, Folaranmi Abdulmugni, dake zaune a wurinsu.
Haka kuma an yi nasarar ceto mutane 7 da suka samu nau’ukan raunuka daban-daban daga wurin da al’amarin ya faru a yau Alhamis.
“Yayin da ake ci gaba da gyare-gyaren, tawagar injiniyoyinmu na shirin fara aiki akan layin 330KkV na biyu.” In ji Mbah.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da rike mukamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo kasar.
A ranar 24 ga watan Oktoban da muke ciki ne Majalisar Dattawan ta karbi bukatar neman tabbatar da nadin sabbin ministoci da ya tura sunayensu .
‘Yan sanda sun tabbatar da cewar ana samun ci gaba a karar da suka shigar ta dan Majalisar Wakilai Alex Ikwechegh, da ake zargi da cin zarafin direban motar haya Stephen Abuwatseya.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.