Tsohon dan Majalisar Wakilan Amurka Matt Gaetz ya janye sunansa daga jerin wadanda zababben Shugaba Donald Trump zai zaba a matsayin antoni janar a yau Alhamis.
Taron zai samu halartar mutane sama da dubu 1 da suka hada da masu baje kolin hajarsu, masu zuba jari daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su daga kasashen Afirka, Turai, Asiya, da Amurka.
Ana tuhumar Ekpa ne tare da wasu mutanen 4 da zargin daukar nauyin laifuffukan ta’addanci, a cewar sanarwar da ‘yan sandan kasar Finland suka fitar a yau Alhamis.
Malamai da masu kare hakkin ‘dan Adam a Najeriya sun fara maida martani akan matakin da Gwamnatin jihar Neja ta dauka na dakatar da wani malamin addinin Musulunci daga yin wa’azi saboda dalilai na yunkurin ta da tarzoma a tsakanin jama’a
Haka kudirin ya nemi a ba da damar gudanar da dukkanin zabubbukan kasar a rana guda.
Majalisar Dattawan, karkashin jagorancin mataimakin shugabanta, Barau Jibrin, ta amince da bukatar karbo rancen ne bayan da kwamitinta akan rancen cikin gida dana ketare da Sanata Magatakarda Wammako ke jagoranta ya gabatar da rahotonsa.
Najeriya ta karbi bakuncin taron hako ma'adinai na shekara-shekara a babban birnin kasar cikin wannan makon domin tattauna hanyoyin zuba jari da matakan da ake bukata don bunkasa fannin.
Kasa da sa’o’i 48 da sanarwar gargadi da babban bankin Najeriya ya yi game da hanyar damfara da sunan tsarin SWFT code na tura kudi tsakanin ‘yan kasuwan kasa da kasa, masana tattalin arziki suna gani akwai mafita.
An sallame shi saboda zargin aikata almundahana.
Kudirin neman yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima da kuma samar da damar yin zabe daga wajen kasar ya tsallake karatu na 2 a Majalisar Wakilai a yau Laraba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wani tsoho dan Jamhuriyar Nijar mai shekaru 58 da haihuwa da ake zargi da safarar makamai daga kasar Aljeriya zuwa Najeriya tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda 16.
Duk da cewa babu tabbatarwa a hukumance game da yawan mutanen da suka mutu, majiyoyi sun ce an hallaka kimanin sojoji 20.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.