Akalla mutane 100 ne, akasarin su mata suka bace, bayan da jirgin ruwan dake dauke da su zuwa wata kasuwar hatsi, ya nutse a ruwa, a yankin kogin Naija dake Arewacin Najeriya, cewar mahukunta a ranar Juma’a.
Jirgin ruwan ya dauki pasinjojin ne daga jihar Kogi ta kan ruwan zuwa makwabciyar jihar ta Naija da sanyin safiyar ranar Juma’a, a lokacin da ya nutse a ruwa, kamar yadda mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Naija, Ibrahim Audu ya shaidawa kafar labarum Associated Press.
Akallah mutane 8 ne aka tabbatar da mutuwar su a wurin, yayin da masu nitso a ruwa ke ta kokarin ceto saura, kamar yadda kafar talabijin din Channels ta ruwaito daga shaidun gani da ido.
Hukumomi dai basu tabbatar da dalilin da ya haifar da nutsewar jirgin a ruwa ba. To sai dai duk da haka, kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa, jirgin ruwan na dauke ne da pasinjoji har 200, dake nuna yuwuwar yi masa lodin da ya fi karfin shi. Ko a kan hanyoyin Najeriya, ababen hawa kan cunkushe sakamakon rashin kyaun hanya, da kan tilastawa masu ababen hawa da dama bin hanyoyin akan tilas.
Har yanzu dai Jami’ai a jihar Kogi basu kai ga gano daidai inda lamarin ya faru ba, suna kuma neman agaji daga sauran hukumomi, cewar, Justin Uwazuruonye, wanda shine shugaban sashen aiyuka na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a jihar.
Irin wanann mummunan lamari na cigaba da faruwa da zama abun damuwa a Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Afrika, a yayin da hukumomi ke fadi tashin ganin an samar da matakan kariya da tsare tsaren sufurin ruwa.
Ana dai danganta hadurran da daukar mutne fiye da kima, da rashin kula da lafiyar jiragen ruwan, da yawancin su kirar hannu ne da aka gina su yadda zasu rika dibar pasinjoji da dama, da kin bin matakan kariya.
Hukumomi sun gaza tilasta yin amfani da rigar kariya ta tsaron rai a yayin irin wadannan tafiye tafiye ta ruwa, yawanci saboda rashin wadatar su ko kuma tsadar su.
Dandalin Mu Tattauna