Binciken da aka gudanar akan shafin dake bada bayanai akan babban layin lantarkin na Najeriya (niggrid.org), ya nuna cewa da misalin karfe 11.30 na safiya yawan lantarkin dake kan babban layin ya sauka gaba daya al’amarin da ya shafi ilahirin kamfanonin dake samar da lantarkin a fadin kasar.
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bada makamancin wannan umarni a sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar.
Sabon farashin mitocin zai fara aiki ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwambar da muke ciki, a cewar sakonnin da kamfanonin rarraba hasken lantarkin suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.
An gudanar da gwajin lafiya ga masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagarin da aka sako din tare da basu shawarwari akan yadda zasu zamo mutane nagari da zasu amfani kansu dama al’umma baki daya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shiga sahum sauran Shugabannin duniya wajen taya Trump murnar sake zabensa a matsayin Shugaban kasar Amurka na 47.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar cewa Janar Lagbaja dan shekaru 56, ya rasu ne ranar Talata a birnin Legas bayan fama da rashin lafiya
Mai bai wa shugaban kasa shawara na kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya tabbatar da faruwar lamarin da ya gudana a fadar shugaban kasar.
Wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta yi watsi da karar da ake tuhumar gomman kananan yaran nan da ake zargi da laifin cin amanar kasa wadanda aka tsare na kusan kwana casa’in sakamakon shiga zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa inda suka daga tutar kasar Rasha
Tinubu ya kuma ba da umarnin a tabbatar an mayar da dukkan yaran ga iyayensu cikin koshin lafiya da aminci.
An gudanar da wannan kame ne sakamakon samamen da aka kai kan wani gini a unguwar Jahi, dake birnin Abuja, inda rahotanni suka ce mutanen na amfani da komfutoci da na’urorin zamani wajen aikata laifuffuka,” a cewarsa.
A cikin wani dogon sakon daya wallafa a shafinsa na X, dan takarar shugaban kasar karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasar da ya gabata ya wallafa cewa zai fara ne da magance matsalar cin hanci da rashawa a matsayin wani bangare na manufarsa akan batun janye tallafin man fetur.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.