Al'amarin ya faru ne da yammacin ranar 10 ga watan Nuwanbar da muke ciki, da misalin karfe 9.30 na dare, a cewar sanarwar rundunar 'yan sandan jihar.
‘Yan sandan lardin Providence sun kama tare da tuhumar Olawusi da laifin cin zarafin yaro karami a ranar 20 ga watan Afrilun 2017. An sakeshi a wannan rana sai dai ya arce daga bisani.
Mutane shida, wanda akasarin su matasa ne, suka rasa rayukansu a wani hadari da ya afku a wurin hakar ma'adinai a kauyen Kilasau dake yankin Rukuba a karamar hukumar Bassa dake jihar Filato
Wani rahoto da ofishin kula da basussuka da kuma rance a Najeriya DMO, ta fitar, ta ce bashin da ake bin kasar a karshen watan Yunin shekarar 2024, ya haura dalar Amurka biliyan 42.9, kwatankwacin Naira tiriliyan 71,826,183,000,000
A yau Talata bikin rantsuwar ya gudana a filin wasan Samuel Ogbemudia da ke Birnin Benin, fadar jihar Edo, watanni biyu bayan da jam’iyyar APC ta lashe zaben da aka gudanar a jihar.
Kwararru a fannin lafiya sun koka cewa, marasa lafiya da dama basu zuwa asibiti sai cutar da su ke fama da ita ta ta’azzara sabili da matsanancin kuncin rayuwa.
A jawabinsa ga taron kolin kasashen Larabawa da Musulmi wanda aka shirya da nufin magance halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, Tinubu ya bayyana matukar damuwa game da yanayin ayyukan agaji da Gaza ke ciki.
Hukumar kafa shingen yaki da hamada ta Najeriya da ake kira Great Wall da turanci, ta ce za ta raba irin dibino miliyan 5 mai samar da yabanya sau biyu a shekara.
Hakan na kunshe n a cikin sanarwar da mai rikon mukamin mataimakin daraktan hulda da jama’a ma burged ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya rabawa manema labarai.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana niyyar ta fara samar da wutar lantarki na tsawon sa'o'i 20 a kullum, zuwa nan da shekara 2027.
A farkon makon da muke ciki ne NUPENG ta shigar da korafi ga gwamnatin tarayya, tare da yin gargadin daukar mataki matukar aka yi amfani da sojoji ko wasu wajen korar mambobinta ko ma’aikatan wucin gadi, da kuma kin mutunta yarjejeniyar da bangarorin 2 suka kulla cikin aminci.
FRSC ta yi wannan kira ne bayan da ta kammala gangaminta na wayar da kan al’umma a kan watannin karshen shekara.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.