Shugaba Joe Biden na Amurka ya jajanta game da iftila’in ambaliyar ruwan baya-bayan nan da ta shafi yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Dangote, wanda ke jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare.
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gaggauta aikin gyara domin dawo da hasken lantarki ga shiyar arewacin Najeriya.
An kama wadanda ake zargin ne a wani wurin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya dake yankin Rafin-Gabas, Agwada, a karamar hukumar Kokona ta jihar.
Kamfanin fasahar hada-hadar kudi na Moniepoint mai tushe a Najeriya ya tara dala miiyan 110 daga kudaden da masu zuba jari ciki harda kamfanin Google suka zuba da nufin bunkasa hada-hadar kudin na’ura da samarwa harkar bankin mafita a fadin Afrika, a cewar Moniepoint a yau Talata.
Bangaren sojin sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Hadin Kai” ya hallaka dimbin ‘yan ta’adda a yankuna 2 na garin Bula Marwa dake jihar Borno.
Yanzu dai kimanin makonni biyu kenan babu hasken wutar lantarki a daukacin yankin na arewacin Najeriya birni da karkara.
Yanzu dai da wannan hukuncin na kotun daukaka kara karo na biyu, kotun koli ce kawai ta yi saura ta yi nata hukunci a kan karar.
Madrid da 'yan wasanta baki daya ba su halarci bikin ba, sannan sun shiga shafukan sada zumunta sun rubuta kalaman da suka nuna bacin ransu saboda ba a zabi Vinicius Jnr ba.
A yau Litinin ne Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da yaki da mabarata, inda ya bayyana cewa jami'an tsaro za su fara kama su daga yau idan sun sake fitowa bara a titunan babban birnin.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a yau Litinin, direban bolt Stephen Abuwatseya ne ya shigar da korafi kan batun ga rundunar.
Ganawar wani bangare ne na kokarin da kungiyar gwamnonin arewa ke yi na tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin dake damun yankin musamman matsalar tsaron da taki ci taki cinyewa, da talauci da yara marasa zuwa makaranta da sauran kalubalen zamantakewar dake addabar yankin
Domin Kari
No media source currently available