Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da rike mukamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo kasar.
A ranar 24 ga watan Oktoban da muke ciki ne Majalisar Dattawan ta karbi bukatar neman tabbatar da nadin sabbin ministoci da ya tura sunayensu .
‘Yan sanda sun tabbatar da cewar ana samun ci gaba a karar da suka shigar ta dan Majalisar Wakilai Alex Ikwechegh, da ake zargi da cin zarafin direban motar haya Stephen Abuwatseya.
Garima ya bayyana mamaki yadda mamallakin matatar man Dangote yace dillalan man na kauracewa matatarsa ta hanyar shigo da fetur din daga ketare.
Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da Babban Bankin Najeriya daga cigaba da sakin kason kudaden wata-wata ga gwamnatin jihar Ribas.
A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoban da muke ciki, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afrika a tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Majalisar Dokokin jihar Nejan dai ta bukaci Gwamnatin jihar da Hukumar Sojin kasar da su yi duk mai yiwuwa domin kwato wannan daji na horar da sojojin daga hannun 'yanbindigar.
Gwamnatin jihar ta Kano ta ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwambar 2024.
Shugaba Joe Biden na Amurka ya jajanta game da iftila’in ambaliyar ruwan baya-bayan nan da ta shafi yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Dangote, wanda ke jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare.
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gaggauta aikin gyara domin dawo da hasken lantarki ga shiyar arewacin Najeriya.
An kama wadanda ake zargin ne a wani wurin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya dake yankin Rafin-Gabas, Agwada, a karamar hukumar Kokona ta jihar.
Domin Kari
No media source currently available