A Najeriya ana ci gaba da samun bayanai masu cin karo da juna cewa kamfanin man NNPCL ya yi rufa rufa kan fara aikin matatar mai ta Fatakwal, inda wasu ke zargin matatar bata fara tace mai ba.
A yau Juma'a kamfanin NNPCL ya yi karin haske a kan cewa tsohuwar matatar man Fatakwal mai karfin tace ganga 60, 000 a kowace rana da aka farfado da ita a kwanakin nan na aiki ne a kan kaso 90 cikin 100, ba kaso 70 cikin 100 ba kamar yadda kungiyar masu gidajen mai ta Najeriya (PETROAN) ta bayyana ba.
A jiya Alhamis PETROAN ta bayyana cewa karfin aikin matatar man na kan kaso 70 cikin 100, inda ake shirye-shiryen kara shi zuwa kaso 90 cikin 100.
Sai dai, a sanarwar da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, ya fitar a yau Juma’a, yace duk da cewa an kayyade matatar na iya tace ganga 60, 000 ce a kowace rana, yanzu tana aiki ne akan kaso 90 cikin 100.
Haka kuma kamfanin ya yi karin haske a kan zargin da wani mazaunin yankin, Timothy Mgbere, ya yi na cewa babu wani abin murna game da matatar, inda yace hade-hade kawai take yi kuma tsohon kaya take fitarwa.
A Talatar da ta gabata NNPCL ya ayyana cewa matatar man Fatakwal ta fara tace danyen mai.
Saurari cikakken rahoton wakilnmu na yankin Neja Delta Lamido Abubakar Sakkwato:
Dandalin Mu Tattauna