Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kara Yawan Man Da Take Hakowa A Kowace Rana


Malam Mele Kyari Shugaban NNPC
Malam Mele Kyari Shugaban NNPC

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce a ranar Alhamis ya kara yawan man da ake hakowa zuwa ganga miliyan 1.8 a kowace rana tare da yiyuwar adadin ya kai miliyan biyu a karshen shekara

An kiyasta yawan man da ake hakowa a kasar da ke kan gaba wajen fitar da danyen mai a nahiyar Afirka ya kai ganga miliyan 1.3 a kowace rana a watan Oktoba, a cewar sabon rahoton kungiyar OPEC.

Najeriya sau da yawa tana kididdigar yawan haƙon gangan man na kusan 250,000 a rana a matsayin wani bangare na karin samu.

Kamfanin na NNPC ya ce an samu karin ne sakamakon hadin gwiwa da hadin hannun kamfanoni abokan huldar masu raba hannun kwangilar kayan masarufi, tare da hukumomin tsaro da gwamnati.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Shugaban kamfanin na NNPC Mele Kyari ya shaida wa manema labarai cewa, “Kungiyar ta yi babban aiki wajen tafiyar da wannan aiki na ba wai ka dai da farfadowar samar da kayayyaki ba, har ma da habaka samar da kayayyaki da matakan da ake sa ran za su kasance cikin kankanin lokaci da kuma dogon zango da masu hannun jarin za su amince da su,” in ji shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG