Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabin Lassa: Gwamnatin Oyo Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4


Beraye ne ke kawo cutar zazzabin lassa
Beraye ne ke kawo cutar zazzabin lassa

Wadanda suka mutun sun hada da maza 3 da wata mata mai shekaru 32 dake shirye-shiryen yin aure.

Ma’aikatar lafiyar Oyo ta rufe wasu asibitoci 2 a karamar hukumar Saki ta Yamma ta jihar sakamakon barkewar cutar da ake zargin zazzabin lassa ce.

Hakan ya biyo bayan tabbatar da mutuwar mutane 4 da kwamitin karta kwana na ma’aikatar wanda ya ziyarci wurin da al’amarin ya faru sakamakon kiran gaggawa da ya samu daka mazauna yankin da suka kira mace-macen da al’amari mai daure kai, ya yi.

Wadanda suka mutun sun hada da maza 3 da wata mata mai shekaru 32 dake shirye-shiryen yin aure.

Sanarwar hadin gwiwar da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a da takwaransa na lafiya suka fitar, tunda fari ta tura kwamitin karta kwanan na jihar Oyo zuwa saki, sakamakon samun dimbin kiraye-kiraye daga karamar hukumar Saki ta Yamma dake bada rahoton barkewar cutar data haddasa mace-mace.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG