Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPCL Ya Kulla Yarjejeniyar Samar Da Iskar Gas Ta Shekaru 10 Da Matatar Dangote


Kamfanin Mai Na Aliko Dangote
Kamfanin Mai Na Aliko Dangote

A cewar NNPCL, hadin gwiwar wani muhimmin mataki ne na tabbatar da nasarar dorewar ayyukan matatar ta Dangote tare da inganta amfani da iskar gas a cikin Najeriya.

Kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL) ya sanar da cewa reshensa dake harkar cinikayyar iskar gas (NGML), ya yi nasarar kulla wata yarjejeniyar cinikyar gas (GSPA) tsakaninsa da matatar man Dangote da sarrafa sinadarai (FZE).

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da babban jami’in yada labaran NNPCL, Olufemi Soneye, ya fitar a jiya Laraba.

A cewarsa yarjeniyar, da Manajan Daraktan, NGML, Barista Justin Ezeala da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote suka rattabawa hannu a shelkwatar kamfanin Dangoten dake unguwar Falomo ta jihar Legas, ta zayyano batun samar da iskar gas domin samar da lantarki da sauran makamashi a matatar ta Dangote, dake yankin Ibeju-Lekki, na jihar Legas.

Dangote
Dangote

A karkashin sharudan yarjejeniyar, NGML zai samar da cubic feet miliyan 100 na iskar gas a kowace rana, za’a samar da cubic feet miliyan 50 na iskar gas babu yankewa a kullum sannan ragowar za’a rika samar da ita a yanyanke ga matatar tsawon shekaru 10 na farko, tare da zabin sabuntawa da bunkasawa.

A cewar NNPCL, hadin gwiwar wani muhimmin mataki ne na tabbatar da nasarar dorewar ayyukan matatar ta Dangote tare da inganta amfani da iskar gas a cikin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG