A sanarwar da ya fitar a yau Talata, janar manajan sashen hulda da jama'a na TCN, Ndidi Mbah, yace wani bangare na tsarin samar da lantarkin ya samu matsala, a ranar Litinin 14 ga watan Oktoban da muke ciki da misalin karfe 6. 48 na yamma.
Farfesa Mamman ya bayyana cewar sabuwar manhajar zata warware matsalolin koyo da koyarwa dana samun aikin yi kasancewar sabon tsarin koyar da sana’o’in da aka kirkiro zai yi matukar tasiri wajen koyawa dalibai sana’o’in zamani.
CAF ta wallafa sabon jadawalin gasar a shafinta na X a yau Talata, sai dai, bai hada dana karawar Najeriya da kasar Libya ba.
An samu karin kaso 0.55 cikin 100 daga hauhawar kaso 32.15 cikin 100 da aka gani a watan Agustan daya gabace shi.
Wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar, ya bayyana cewa 1 daga cikin kowadanne yara mata 8 a duniya suna fuskantar hadarin cin zarafi da fyade. Daya daga cikin matan 5 kuma suna fuskantar irin wannan barazana ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani, wanda adadinsu ya kai miliyan 650.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na daren ranar Juma’a, sa’adda ‘yan bindigar suka shiga garin inda kai tsaye suka nufi gidan basaraken mai suna Alhaji Tanimu Garba, suka kuma harbe shi har lahira.
Ezeh ya ce "lamarin ya shafi duk tashoshin TCN a fadin kasar, saboda haka babu wadatar wuta da za'a baiwa abokan hulda."
Bayan nasarar da Najeriya ta samo a kan Libya a Juma’ar data gabata, an tsara cewa zasu sake karawa a birnin Benghazin Libya a gobe Talata, a ci gaba da gasar neman cin kofin nahiyar Afirka na 2025.
A jawabinsa yayin karo na 30 na taron kolin Najeriya a kan tattalin arziki daya gudana a Abuja, Ministan Kasafi Da Tsare-Tsare, Atiku Bagudu, ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa duk da halin matsin da ake fama da shi a kasar, akwai fatan samun sauki a nan gaba.
Bene ya ruguje ne da safiyar yau Litinin a yayin da mutane ke shirye-shiryen fara gudanar da harkokinsu.
A kudirin da ya fito daga bangaren zartarwa, majalisar na neman a kara harajin zuwa kaso 10 cikin 100 a shekarar 2025.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.