Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsayawar Babbar Tashar Wutar Lantarki Ta Najeriya Ya Jefa Daukacin Kasar Cikin Duhu


Tashar wutar lantarrki a Najeriya (Facebook/ Ministry of Power Nigeria)
Tashar wutar lantarrki a Najeriya (Facebook/ Ministry of Power Nigeria)

Ezeh ya ce "lamarin ya shafi duk tashoshin TCN a fadin kasar, saboda haka babu wadatar wuta da za'a baiwa abokan hulda."

Rahotanni daga Najeriya sun bayyana cewa an sami tangarda ta tsayawar tsarin samar da wutar lantarki na kasar, sakamakon lalacewar babbar tashar samar da lantarkin.

Wata sanarwar da aka rabawa manema labarai ta adreshin yanar gizo, mai dauke da sa hannun kakakin kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu Emeka Ezeh, ta ce lamarin ya auku ne da misalin karfe shida da minti arba'in da biyar na yammacin ranar Litinin.

Ezeh ya ce "lamarin ya shafi duk tashoshin TCN a fadin kasar, saboda haka babu wadatar wuta da za'a baiwa abokan hulda."

Ya kara da cewa "wannan lalacewar ta tsarin wutar lantarkin shi ne karo na shida a wannan shekara, kuma tsayawar aikin tsarin ya haifar da duhu a yawancin yankunan kasar baki daya.

Alkaluman da Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya, NAN ya fitar, sun nuna cewa ma'aunin wutar lantarki na kasar ya durkushe kusan sau 227 a cikin shekaru 14 da suka gabata.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka kara kudin wutar lantarki a watan Afrilu da kashi 240 cikin 100, wanda ya kara dagula wahalhalun da ' yan Najeriya ke fuskanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG