'Yan-Najeriya na ci gaba da tattaunawa akan kalaman mai-baiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara akan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da ya ce wasu jami'an tsaron Najeriya suna sayarwa 'yan-bindiga makamai.
Masana da mahukunta sun ce Hukuncin da babbar kotu ta yanke na haramtawa hukumar VIO tsarewa ko kuma cin tarar direbobin motoci a birnin tarayya Abuja, ya kawo cikas ga harkokin su na samun kudadden shiga da kuma kaiwa ga kara yawan direbobin dake saba ka’idar tuki a Abuja.
Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis lokacin da ya kaiwa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ziyara a fadarsa dake gidan Sir Kashim Ibrahim, a wani bangare na rangadin da yake yi a yankin arewa maso yamma.
A wani babban al’amarin da ya shafi al’ummar Musulmin Najeriya, an nada Farfesa Ilyasu Usman, dan kabilar Igbo na farko, a matsayin limamin masallacin kasa na Abuja.
Gwamnatocin tarayya da jihohi da kananan hukumomin Najeriya sun rarraba naira tiriliyan 1.298 a tsakaninsu a matsayin kudin shigar da ya taru asusun tarayya a watan Satumbar da ya gabata.
A jawabinsa Shettima yace Najeriya da Sweden na da dadadden tarihin yin hadin gwiwa, musamman a fannonin kasuwanci da fasaha da ci gaba mai dorewa.
A cewar rahoton, an samu kari da mutum miliyan 115 a 2023 zuwa 129 a 2024, abinda ke nufin cewa ‘yan Najeriya miliyan 14 sun kara talaucewa a bana.
A cewar masanin tsaro, Rabiu Ladodo kamata ya yi a yi wa jami'an tsaro adalci domin ba duk bindigar da ke hanun dan ta'adda ne ta jami'an tsaro ba.
Gachagua shi ne mataimakin shugaban kasa na farko da aka taba tsigewa a tarihin Kenya.
Katz ya kwatanta kashe Sinwar a matsayin wata "gagarumar nasara ga sojojin Isra’ila."
Gwamnan ya kuma bayyana cewa a farkon shekarar da muke ciki ma saida jihar ta kara albashin ma’aikatanta, inda ya kara da cewa yana da burin mayar da mafi karancin albashin N100, 000 a watan janairun 2025.
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hadarin tankar dakon man fetur a garin Majiya na jihar Jigawa a Najeriya ya kai kusan 170 yayin da fiye da mutane 60 ke ci gaba da karbar magunguna a asibitoci daban daban.
Domin Kari
No media source currently available