Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya na Najeriya (JOHESU) ta ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7, tun daga tsakad daren yau Juma’a.
Hukumar binciken afkuwar hadura ta Najeriya (NSIB) ta bayyana cewar an gano karin gawawwaki 2 daga jirgin saman shelkwafta kirar Sikorsky S-79 da ya yi hatsari a birnin Fatakwal, fadar gwamnatin jihar Ribas.
Kotun da’ar ma’aikata ta bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an jihar Kaduna guda uku biyo bayan zargen da ake musu na ba da bayanan karya wurin bayyana kadarorinsu, yayin da suke jira su gurfana gaban kotu.
Hukuncin na zuwa ne bayan da a Talatar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya dake Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Simon Amobeda, ta dakatar da gudanar da zabubbukan kananan hukumomi.
Tuni dai Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, suka baro New York zuwa Najeriya.
Kotun kolin ta ba da umarnin cewa za a ci gaba da karbar takardun kudin na naira 200 da 500 da 1000 tare da sabbin da aka sauyawa fasali.
A cewar NNPCL, mutum takwas ne a cikin jirgin wadanda suka hada da fasinja 6 da matuka biyu.
Kalaman Badaru sun zo ne makonni uku bayan Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa karewa.
Daukar wannan mataki a cewar Fadar Shugaban kasar, yunkuri ne na rage kudaden da gwamnati ke kashewa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.
Sanarwar da mahukuntan kasar ta fitar ta ce, jirgin ya kutsa cikin ruwan da ke kusa da Bonny Finima a cikin Tekun Atlantika, kuma ta kara da cewa tuni an fara aikin ceto.
Bukatar Shugaba Tinubu ta neman a gaggauta tabbatar da ministocin na kunshe ne a cikin wasikar da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio wanda ya karantata a farkon zaman majalisar na yau Alhamis
Domin Kari
No media source currently available